7 Janairu 2015 - 11:41
Harin kunar bakin wake a Turkiya mutane biyu sun rasa ransu.

Shugaban yan sanda na Birnin Istanbul dake Turkiya yace; a jiya wata mata wadda tayi jigida da abubuwa masu fashewa sannan ta tayar dasu idan da ta kashe kan ta.

Wasif sahin shugaban yan sandan Birnin Istanbul yace; matar tayi niyar tayar da bam dine a wata matsayar yan sanda dake yanki sultan Ahmad sannan matar tayi nasarar tayar da bam din kafin jami'an tsaro su samu damar cafketa.

Kamfanin Dillancin labarai na Faransa daga Istanbul, harin yayi sanadiyar jikkata wani dan sanda sannan daga baya ya mutu, wani dan sanda kuma ya samu raunuka.

Ruhotannin na nuni da cewa, hadarin ya aukune sakamakon fashewar bam din hannu.ABNA